Home Labarai Iran: Kafafen Yada Labaran Kasar Sun Ce Babu Maƙarƙashiya

Iran: Kafafen Yada Labaran Kasar Sun Ce Babu Maƙarƙashiya

536
0
1400080210375292523889094
1400080210375292523889094

Kafafen yaɗa labaran Iran sun ce babu alamar wata maƙarƙashiya a hadarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban ƙasar a ranar Lahadi,

Rahoton farko daga sojojin ƙasar ya ce, ”babu alamar hujin harsashi ko wani abu mai kama da haka a jikin jirgin, kuma babu wani abin zargi a tattaunawar da aka yi tsakanin matuƙa jirgin da masu kula da tashin jirgin”.

Rahoton ya gano cewa jirgin ya kama da wuta ne bayan ya tokari wani wuri da hazo ya rufe.

Amma har yanzu sojojin na ci gaba da gudanar binciken.

A ranar Alhamis ne aka binne Shugaba Ibrahim Raisi a birnin Mashhad, inda nan ne mahaifarsa.

Leave a Reply