kotun Duniya ta umarci Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa a yankin Rafah na Gaza
Afrika ta Kudu ce ta shigar da ƙarar gaban kotun duniya bisa zargin Isra’ila da take yarjejeniyar kisan kiyashi.
Ta ce shiga tsakanin na da muhimmanci domin tseratarwa da kuma kare rayuwar Falasɗinawa.
Kakakin Isra’ila ya ce babu wani mai iko da zai hana ta kare mutanenta da kuma murkushe Hamas a Gaza.
Kotun ICJ ba ta da ikon tursasawa amma duk wani hukunci da ta yi da bai yi wa Isra’ila dadi ba yana da tasiri a idon duniya.