Ofishin Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa (NSA), ya yi kira da a tilasta bin doka da odar da ke shimfiɗe a ƙarƙashin Dokar Haramcin Hada-hadar Kuɗaɗen Harƙalla ta Hanyar Intanet, dokar da aka fi sani da ‘cybercrime law’.
Ofishin NSA Nuhu Ribadu ya yi wannan kira a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, bayan wani ƙasaitaccen taron Manyan Jami’an Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙarƙashin Ƙasa a Afrika suka gudanar.
Taron dai kamar yadda sanarwar ta bayyana, an gudanar da shi ne a Abuja, tsakanin 22 zuwa 23 ga Afrilu.
Daga cikin manufofi da ƙudirorin da aka cimma bayan taron, sun haɗa da yin kira “a ƙara inganta hanyoyin yaƙi tare da daƙile ayyukan harƙallar kuɗaɗe ta hanyar intanet a Afrika.
Ƙudirin ya kuma haɗa da yin kira ga gwamnatocin Afrika su ƙirƙiro matakan hana amfani da soshiyal midiya da sauran kafafen da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen yaɗa mugayen manufofin su.
Haka dai sanarwar wadda Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Ofishin NSA, Zakari Mijinyawa ta ƙunsa.














































