Home Home INEC Za Ta Yi Haɗaka Da Ƙungiyoyin Sufuri Kan Zirga-Zirga Ranar Zaɓe

INEC Za Ta Yi Haɗaka Da Ƙungiyoyin Sufuri Kan Zirga-Zirga Ranar Zaɓe

47
0
Hukumar Zaɓe Mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta haɗa gwiwa da direbobi mamallakan motocin haya da sauran ma’aikatan tashar mota a jihar Oyo, domin a samo hanyar da za a tafiyar da hada-hadar sufurin mutane da kaya a ranar zaɓe.

Wannan dai shi ne dalilin da ya sanya hukumar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa a kan haka.

Bature Zabe na jihar Oyo Dakta Adeniran Tella da kuma hukumar zaben su ka sanar da haka, jim kaɗan bayan kammala taron ganawa da shugabannin ƙungiyoyin sufuri a Ibadan.

Rahotanni sun ce, taron ya samu halartar ƙungiyoyin sufurin mota da su ka haɗa da NURTW,da NARTO, da RTEAN, da shugabannin gudanarwa na tashar Oyo, da wakilan hukumar tsaro ta farin kaya DSS da sauran su.