Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa da Hukumar Yaki da cin hanci Rashawa EFCC da sauran masu ruwa da tsaki, sun fara wani zama domin tattauna batun rashawa da aka samu a zaben shekara ta 2023.
Tawagar, wadda cibiyar ‘The Conversation Africa’ ke ɗaukar nauyi, ta tsara gudanar da irin wadannan tarurrukan ne domin tattauna tsarin shugabanci.
Wata Sanarwa da tawagar ta fitar, ta ce sauran mutanen da ake zama da su sun hada da kungiyoyin fararen-hula da kungiyar Code 4 Afrika da dai sauran su.
Ana dai sa ran bayan zaman za a fito da batutuwan zarge-zargen da ake yi a kan rawar da rashawa ta taka a zaɓen shekara ta 2023 da sauran duk wasu abubuwan da ake zargi.