Home Labaru Ilimi Ilimi: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirinmaida Kwalejin Kimiyya Ta Kaduna Zuwa...

Ilimi: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirinmaida Kwalejin Kimiyya Ta Kaduna Zuwa Jami’a

734
0

Majalisar dattawa ta yi zama na uku a kan kudurin maida kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna zuwa cikakkiyar Jami’ar Birnin Kaduna, wato City University of Technology a turance.

Hakan dai, ya biyo bayan nazarin da kwamitin asusun tallafa wa manyan makarantu na majalisar dattawa a karkashin jagorancin Sanata Jibrin Barau ya yi a kan Kudurin da Sanata Shehu Sani ya kai.

Ana sa ran majalisar dattawa za ta tura kudurin zuwa ga majalisar wakilai domin su sanya hannu kafin a gabatar da shi a gaban shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu sannan ya zama doka. Bangaren ilimi dai na ci-gaba da samun kalubale a Nijeriya, musamman makarantun gaba da sakandare, wadanda ba wuya ma’aikatan su ke shiga yajin aiki saboda wasu bukatun su.