Home Labaru Ilimi Ilimi: Buhari Ya Amince A Biya Kungiyar ASUU Naira Biliyan 25- Minista

Ilimi: Buhari Ya Amince A Biya Kungiyar ASUU Naira Biliyan 25- Minista

288
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a biya malaman jami’o’in hakkokin su da alawus-alawus din su na naira biliyan 25.

Idan dai ba a manta ba, wadannan kudade na daga cikin sharuddan janye yajin aiki da malaman suka gindaya wa gwamnatin tarayya a yayin da suka kulla yarjejeniya game da kin sake shiga yajin aiki.

Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya sanar da haka a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce baya ga naira biliyan 25, gwamnatin ta rarraba wa jami’o’in Nijeriya naira biliyan ashirin a shekarar da ta gabata.

A cewar ministan, dukkanin jami’o’in gwamnati sun ci moriyar wadannan kudade naira biliyan 20, kuma gwamnati za ta cigaba da kokarin cika duk wata yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar ASUU, duk da cewa ta tarar da bashin naira Tiriliyan 1 da biliyan 3 da ASUU ke bin gwamnatocin baya.

A karshe ministan ya ce, sun kashe naira Tiriliyan 1 da biliyan 38 a fannin ilimi a Nijeriya ta hanyar bada tallafin TETFund da kuma hukumar ilimi ta bai daya UBEC, inda ya ce an kuma gudanar da manyan ayyuka da wadannan kudade.