Home Labaru Iftila’I: Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum 5 A Jihar Yobe

Iftila’I: Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum 5 A Jihar Yobe

71
0
Ambaliyar-ruwa

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Yobe sun tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da gawarwaki biyu suka bace sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a Karamar Hukumar Potiskum.

Aminiya ta ruwaito cewa, ambaliyar ruwan ta auku a sassa da dama na garin Potiskum biyo bayan mamakon ruwan sama da aka tafka a daren Lahadi.

Wani mazaunin yankin mai suna Hamza Maidede, ya ce gine-gine da yawa a kewayen al’ummomin Nahuta sun rushe tare da karin wasu kadarori da dama da suka salwanata.

Maidede ya ce A halin yanzu suna cikin bakin ciki saboda wani jariri a unguwar ya rasa ran sa yayin da gini ya rufta a kan sa.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dokta Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce a halin yanzu tawagar bincike da aikin ceto na SEMA suna Potiskum inda suke gudanar da bincike tare da taimaka wa al’umma a kokarin gano gawarwakin da suka bace.

Goje ya kara da cewa, ana ci gaba da aiwatar da wani shiri na sauya matsugunin mazauna yankuna da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a Damaturu kamar yadda gwamnan jihar ya umarta.