Tsohon Gwamnan jihar Ondo Cif Bode George, ya lashi takobin cewa idan har Bola Tinubu ya zama Shugaban kasa zai kwashe kayan sa ya bar Nijeriya kwata-kwata.
Bode George ya bayyana haka ne, a wata tattaunawa da yay i da jaridar Vanguard, inda ya ce Tinubu ba irin mutumin da za a mika wa mulkin Nijeriya ba ne domin kashe ta zai yi.
Ya ce Tinubu ba irin mutumin da za a damka wa amanar babbar kasa kamar Nijeriya ba ne, don haka kamata jama’a su su maida hankali a kan wanda zai jagorance su.
Bode George ya kara da cewa, mutanen da ke goyon bayan Tinubu kawai wadanda ke amfana da kudin sa ne.