Home Labarai Idan Aka Rantsar Da Tinubu To An Yi Dagadaga Da Dimokuraɗiyya a...

Idan Aka Rantsar Da Tinubu To An Yi Dagadaga Da Dimokuraɗiyya a Najeriya – Datti Baba-Ahmed

1
0

Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour
Datti Baba Ahmed, ya gargaɗi shugaba Buhari da babban
jojin Nijeriya su tabbatar ba a rantsar da Tinubu a matsayin
shugaban Nijeriya ba.

Idan ba a manta ba, Tinubu ya lallasa abokan takarar sa na
PDP Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar Labour,
amma tun bayan sanar da sakamakon zaɓen su ka lashi
takobin kalubalantar zaɓen a kotu.

A wata hira da Datti Ahmed ya yi da Talabijin na Channels,
ya gargaɗi shugaban kasa da babban jojin Nijeriya kada su
kuskura su rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya
domin bai cancanta ba.

Datti Ahmed, ya ce idan aka kuskura aka rantsar da Tinubu
dimokraɗiyya ta zama gawa a Nijeriya, kuma ba za su yarda
da hakan ba.