Gwamnatin jihar Kaduna ta sa dokar hana fita ta Sa’o’i 24 a
unguwannin Sabon Garin Nassarawa da Tirkaniya da ke
yankin ƙaramar hukumar Chikun.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran
cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ya ce an
ɗauki matakin ne bayan wani rikicin ‘yan sara-suka ya yi
sanadiyyar mutuwar mutane biyu.
Sanarwar, ta umarci jami’an tsaro su tabbatar da dokar a
unguwar, domin maido da zaman lafiya yayin da ake ci-gaba
da bincike don gano musabbabin abin da ya haddasa hargitsin.
Kwamishinan tsaron ya yi kira ga mazauna yankin su yi
biyayya ga dokar, wadda ta fara aiki nan take.
You must log in to post a comment.