Home Labaru Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara: Gwamnati Ta Sanar Da Ranakun Litinin...

Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara: Gwamnati Ta Sanar Da Ranakun Litinin Da Talata

216
0

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 27 da Talata 28 ga watan Disamba a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirsimeti, yayin da ranar 3 ga watan Junairun 2020 a matsayin hutun sabuwar shekara.


Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin Najeriya.
Ya kuma mika sakon fatan alheri ga ‘yan Najeriya na ciki da mazauna kasashen waje a lokacin bukukuwan Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da Sakataren ma’aikatar cikin gida Shu’aibu Belgore ya aike wa manema labarai.
Sanarwar ta ambato Mista Aregbesola na kira ga mabiya addinin Kirista su yi koyi da rayuwar Isa Almasihu, na son zaman lafiya, da tausayi da yin abin da ya dace a daidai lokacin da suke bikin tunawa da shi.

Leave a Reply