Home Labarai Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 A Jihar Zamfara

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 A Jihar Zamfara

189
0

Rahotanni daga kauyen Shemori cikin karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara na cewa ‘yan bindiga sun sace mutum 13 ciki har da mata a jiya da daddare.


Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun auka wa kauyen ne sakamakon gaza biyan harajin da suka dora musu.
Shaidun da majiyarmu ta zanta da su ta waya daga kauyen na Shemori sun ce a daren jiya ne maharan suka shiga garin a kan Babura.
Wani mazaunin kauyen ya ce ‘yan bindigar sun auka musu ne sakamakon kin biyan harajin da suka saka musu a kwanakin baya.
Sai dai ya ce babu wanda ya rasa ransa, amma sun yi wa wani mutum dukan tsiya saboda ya yi yunkurin tserewa.
Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta tabbatar da aukuwar harin, inda kakakin rundunar SP Muhammad Shehu ya ce jami’ansu na can na kokarin kubutar da su.

Leave a Reply