Home Labaru Sadarwa: Gwamnati Ta Amince Da Karin Wa’adin Hada Layukan Waya Da Lambar...

Sadarwa: Gwamnati Ta Amince Da Karin Wa’adin Hada Layukan Waya Da Lambar Katin Dan Kasa.

341
0

Ministan sadarwa da tattalin arziki Isa Ali Pantami ya amince da tsawaita wa’adin aikin hada layin waya da lambar zama dan kasa wato NIN wanda ke karewa yau laraba 30 ga watan Disambar shekarar 2020.

Anata bangaren babbar jami’ar hukumar bada katin Dan kasa Hajiya Hadiza Ali Dagabana tace  an kara lokacin yin wannan aiki zuwa ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2021 mai kamawa.

Ta ce ma’aikatan hukumar zasu ci gaba da aiki dare da rana a jihohin kasar nan domin tabbatar da an yi musu rajista.

Zalika ta bukaci wadan basu mallaki katin zama Dan kasa ba, da su tabbatar sun yi kafin lokacin da aka kayyade na ranar 9 ga watan Faburairun 2021.

Daga bisani ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi kokari su yi rajistan lambobin wayoyin su kafin ranar 19 ga wata Janairun shekarar 2020.