Home Labaru Kasuwanci Hukumar Tara Haraji Za Ta Bi Diddigin Waɗanda Aka Lissafa

Hukumar Tara Haraji Za Ta Bi Diddigin Waɗanda Aka Lissafa

14
0
FIRS

Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa, ta ce za ta bi diddigi ta kuma hukunta duk ‘yan Nijeriyar da aka kama sun karya dokar biyan haraji a cikin harƙallar ‘Pandora Papers.’

A Cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar Johaness Woluola ya fitar, ya ce hukumar za ta bi duk mutanen da ta lissafa sun karya dokokin biyan haraji domin a hukunta su.

Daga cikin wadanda aka lissafa kuwa akwai tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi, da Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, da Sanata Stella Oduah, da Shugaban Riƙo na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa Bello Koko, da Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun da wasu makusantan su.

Bello Koko dai shi ne ma’aikacin gwamnatin da Shugaba Buhari ya amince a naɗa shi riƙon Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa bayan an cire Hadiza Bala Usman.

Wata majiya ta ce, Bello Koko ya shiga cikin ƙamayamayar karkatar da kuɗaɗen Nijeriya zuwa kasashen ketare, inda ake zargin shi da sayen manyan gine-gine da kadarori a birnin London.