Home Labaru Kasuwanci Shugaba Buhari Ya Samu Sahalewar Majalisar Dattawa

Shugaba Buhari Ya Samu Sahalewar Majalisar Dattawa

16
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai iya ci-gaba da kinkimo basussuka saboda Nijeriya ta na bukatar kudi a halin yanzu.

Sanata Ahmad Lawan, ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa su ke amincewa a duk lokacin da Shugaban kasan ya nemi izinin karbar bashi.

Ahmed Lawan ya bayyana haka ne, lokacin da Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi na shekara ta 2022 a zauren majalisar.

Ya ce shugaba Buhari ya yi alkawari Gwamnatin sa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki, shi ya sa majalisa da bangaren zartarwa su ka yanke shawarar a daina ba ma’aikatun da ke kin shigar da kudin shiga na shekara ta 2022 wasu kudade.

Sanatan ya cigaba da cewa, ya zama wajibi gwamnati ta karbo basussuka daga gida da kasashen ketare, domin gudanar da ayyuka a fadin Nijeriya.