Home Labaru Kiwon Lafiya Hatsarin Mota: Mutum 9 Sun Rasa Ransu A Jihar Kano

Hatsarin Mota: Mutum 9 Sun Rasa Ransu A Jihar Kano

812
0

Hukumar Kiyaye Haɗura ta kasa reshen Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum 9 a wani hatsarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Kano.

Shugaban hukumar a Kano Zubairu Mato ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, inda ya ce wasu mutum uku sun ji munanan raunuka a hatsarin da ya faru a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Ngigeria NAN ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne yayin da wasu motoci biyu suka haɗu a garin Imawa na Ƙaramar Hukumar Kura dake Jihar ta Kano.

Har ila yau Kwamandan ya alaƙanta hatsarin da tukin gangancin masu tuka motocin suke yi a lokacin da lamarin ya faru, a yayin da dukkaninsu ke ƙoƙarin wuce babur ɗin da ke wani ɓangare na titin.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai maza biyu da mata shida da kuma yaro ɗaya.

Leave a Reply