Rundunar sojan sama ta Nijeriya, ta tabbatar cewa matuƙa jirgin ta biyu ne su ka rasu a hatsarin da jirgin su ya yi a Jihar Kaduna.
Jirgin dai ya faɗo ne da yammacin ranar Talatar da ta gabata, a
wani sansanin sojin saman kuma duk mutum biyun da ke ciki ne
su ka rasu.
Rundunar ta bayyana cewa, sunan dakarun su ka rasa rayukan su
sun hada da Laftanar Abubakar Muhammed Alkali da Laftanar
Elijah Haruna Karatu.
Tuni dai Hafsan Sojin Sama na Nijeriya Air Marshal Oladayo
Amao ya kai ziyara wajen da hatsarin ya faru domin jajenta wa
dangin mamatan.
Kakakin rundunar Edward Gabkwet, ya ce za su yi natsattsen
bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.














































