Home Labarai Maslaha: Ana Kan Yinkurin Sake Hada Kan Bangarorin Izala Wuri Guda

Maslaha: Ana Kan Yinkurin Sake Hada Kan Bangarorin Izala Wuri Guda

111
0

Bayan kwashe tsawon Shekaru da rabuwar kungiyar Izala gida
biyu, wato Bangaren ‘yan Kaduna da Sheik Abdullahi Bala Lau
ke Shugaban ta, da Bangaren ‘Yan Jos da Sheik Sani Yahaya
Jingir ke shugabanta, yanzu haka ana yunkurin hada kan
bangarorin biyu a cikin wannan wata mai na Ramadan.

Idan ba a manta ba, bayan rabuwar kungiyar Izala a shekara ta
1991, an yi nasarar sake hade ta wuri guda a shekara ta 2011,
amma tafiyar ba ta yi nisa ba kowane bangare ya kama gaban sa.

Yanzu haka dai wasu manyan masu fada aji na bangarorin biyu
ne su ka fara yinkurin sake dunkule kungiyar Izalar wuri guda.

Dr. Mustapha Bashir, wanda Babban jigo ne a bangaren Izalar
Jos, ya ce su na da kyakkyawan zato a kan wannan yunkuri.

Leave a Reply