Home Labaru Kiwon Lafiya Hatsari: Mutanem 7 Sun Mutu Bayan Shaƙar Iska Mai Guba A Jihar...

Hatsari: Mutanem 7 Sun Mutu Bayan Shaƙar Iska Mai Guba A Jihar Osun

60
0
Gen Kills

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai ‘yan gida ɗaya, sakamakon shaƙar iska mai guba a jihar Osun.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun, ta ce mutane takwas aka samu kwance a ɗakunan su a gidan da su ke, amma mutum ɗaya aka samu ya na numfashi.

Kakakin ‘yan sanda ta jihar Yemisi Opalola ta shaida wa manema labarai cewa, makwabta ne su ka fara fahimtar al’amarin waɗanda su ka yi tunanin dukkan su sun mutu.

Yemisi Opalola, ta ce ‘yan sanda su na gudanar da bincike a kan musabbabin aukuwar al’amarin, sai dai ta ce hayaƙin janareto na iya kasancewa musabbabin kisan.