Home Labaru Harin Zabarmari: Malaman Addinin Musulunci A Najeriya Sun Nuna Gazawar Buhari

Harin Zabarmari: Malaman Addinin Musulunci A Najeriya Sun Nuna Gazawar Buhari

295
0

Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yin sakaci wajen mayar da hankali domin magance matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa.

Malaman sun yi wannan zargi ne bayan wasu ‘yan ta’adda da ake zargi ‘yan Boko Haram ne sun yi wa manoma 43 kisan gilla a jihar Borno.  

Malamai da dama dai da kafar BBC ta tattauna da su, sun ce dole gwamnatin Shugaba Buhari, ta zage damtse domin shawo kan matsalar tsaro in ba haka ba kuma Allah zai yi fushi da ita.

Da yake nuna bacin ran sa fitaccen Malamin addinin Musuluncin Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce ya zama wajibi Shugaba Buhari, ya sauya salo wajen tunkarar matsalar tsaron da ke addabar arewa.

Ya ce a matsayin sun a malamai suna kira ga shugabannin su ji tsoron Allah su san cewa zai tambaye su rayukan mutane miliyan 200 da ke rayuwa a Najeriya, domin alkawari suka yi cewa za su yi iya yin su su ga cewa sun dauki mataki a kan harkar tsaro, da noma da kiwo da kuma cin hanci da rashawa.

Malamin ya ce wadannan abubuwa a yanzu sun kara tabarbarewa da lalacewa ne don haka ya zama wajibi a shawo kan su.