Home Labaru Harin Ta’addanci: An Saka Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Tillabery Dake Nijar

Harin Ta’addanci: An Saka Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Tillabery Dake Nijar

191
0
Sojan Nijar 89 Ne Su Ka Mutu A Harin Shinagodar
Sojan Nijar 89 Ne Su Ka Mutu A Harin Shinagodar

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya jagoranci taron gaggawa na kwamitin tsaro na ƙasar inda suka tattauna kan matsalolin tsaro a ƙasar musaman a Jihar Tillabery.

Daga cikin matakan da zaman ya ɗauka akwai batun sa dokar ta-ɓaci a faɗin jihar ta Tillabery.

Hakan ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai ranar Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas – ‘yan Nijar biyu da Faransawa shida.