Rahotanni daga Sudan na nuna aƙalla mutum 45, mafi yawan su ƙananan yara da mata ne suka mutu a wani harin jirgi mara matuƙi da aka kai a kan wata motar fasinja a Khartoum, babbar birnin ƙasar.
Jam’iyyar Nation Umma Party (NUP) ta ce, an kai hari kan wata motar fasinja ɗauke da sama da mutum 45 waɗanda suka zo daga birnin Rabak na jihar Nile da jirgi mara matuƙi a yankin Taiba Al-Hassanab.
Sudan dai tana fama da yaƙi a ƙasar, wanda ya kashe mutane da dama, sannan ya raba wasu da muhallan su.