Home Labaru Hare-Hare: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku A Kudancin Kaduna

Hare-Hare: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku A Kudancin Kaduna

68
0
Yan Bindida

Aƙalla mutum uku aka kashe tare da raunata wasu sakamakon wasu hare-hare da aka kai a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Lamarin wanda ya faru ranar Juma’a a ƙauyukan Machun da Manuka, ya biyo bayan kashe mutum biyar da aka yi ne a farkon watan Agusta a yankin.

Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya tabbatar da kai harin cikin wata sanarwa, yana mai cewa maharan sun shiga garuruwan ne suna harbe-harbe a kan mai tsautsayi.

Aruwan ya ce jami’an tsaro sun amsa kiran gaggawa daga garin Machun, inda da isar su wurin suka jiyo ƙarar harbi a ƙauyen Manuka mai maƙotaka.

Sai dai ya ce gawar mutum uku ‘yan sandan suka tarar da kuma adadi mai yawa na waɗanda aka raunata bayan isar su yayin da maharan suka tsere kafin su ƙarasa.