Home Labarai Hare-Hare: Rahotanni Sun Ce An Kashe Mutum 38 Da Kona Gidaje Da...

Hare-Hare: Rahotanni Sun Ce An Kashe Mutum 38 Da Kona Gidaje Da Amfanin Gona A Kaduna

95
0
Rahotani daga Jihar Kaduna na cewa ƴan bindiga sun kashe mutum 38 a Ƙaramar Hukumar Giwa.

Rahotani daga Jihar Kaduna na cewa ƴan bindiga sun kashe mutum 38 a Ƙaramar Hukumar Giwa.

Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ce ta sanar da hakan inda ta ce jami’an tsaro sun ba ta rahoton cewa mutum 38 aka kashe a kauyukan Kauran Fawa da Marke da Riheya da Idasu duk a Ƙaramar Hukumar Giwa.

An kuma bayyana cewa ƴan bindigan sun ƙona gidaje da manyan motocin ɗaukar kaya da ƙananan motoci da amfanin gona.

Tuni dai gwamnan jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai ya bayar da umarni ga hukumar ayyukan gaggawa ta jihar da ta binciki lamarin da kuma kai ɗauki ga waɗanda lamarin ya shafa.