Home Labarai Haraji: Buhari Ya Karɓi Rahoton Kwamatin Yi Wa Tsarin Raba Kuɗin Shiga...

Haraji: Buhari Ya Karɓi Rahoton Kwamatin Yi Wa Tsarin Raba Kuɗin Shiga Kwaskwarima 

109
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karɓi wani rahoton da
ya ba shi shawara a kan yadda za a yi wa tsarin raba kuɗaɗen
shiga tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da ƙananan
hukumomi kwaskwarima.

Wata majiya ta ce, shugaba Buhari ya karɓi rahoton ne a Fadar
Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A Ƙarƙashin tsarin raba harajin da ake amfani da shi a yanzu,
gwamnatain tarayya ta na ɗaukar sama da kashi 52 da rabi cikin
100 na kuɗaɗen da aka raba, yayin da jihohi ke samun sama da
kashi 26 da rabi, sai kuma ƙananan hukumomi da ke karɓar
kashi 20 da rabi cikin 100.

Tun a watan Oktoba na shekara ta 2021, kwamatin ya fara aikin
lalubo hanyoyin yi wa tsarin gyara.