Home Home Har Yanzu Ba A Daƙile Matsalar Tsaro A Najeriya Ba – Tinubu

Har Yanzu Ba A Daƙile Matsalar Tsaro A Najeriya Ba – Tinubu

34
0
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa da aka yi a Jihar Edo, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a daƙile matsalar tsaro a Nijeriya ba.

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa da aka yi a Jihar Edo, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a daƙile matsalar tsaro a Nijeriya ba.

Tinubu ya bayyana haka ne, a ciki wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa Tunde Rahman ya raba wa manema labarai.

A ranar Asabar da ta gabata ne, wasu ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da fasinjoji 31 masu jiran shiga jirgin ƙasa, daga garin Igueben na Jihar Edo zuwa Warri na Jihar Delta.

Bola Ahmed Tinubu, ya ce ganin yadda ‘yan bindiga su ka kwashe fasinjojin jiragin ƙasa su 31 a Jihar Edo, tabbas akwai sauran jan aiki wajen kawar da matsalar tsaro a Nijeriya.