Home Labaru Hangen Nesa: Ya Kamata A Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Nijeriya –...

Hangen Nesa: Ya Kamata A Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Nijeriya – Rahoto

334
0
Agnes Callamard, Sakamakon Farko na Binciken Da Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya
Agnes Callamard, Sakamakon Farko na Binciken Da Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya

Sakamakon farko na binciken da wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya Agnes Callamard ta yi, ya bukaci a gaggauta kawo karshen ta’addanci a fadin Nijeriya.

Agnes Callamard, ta ce Nijeriya ta na fama da ayyukan ta’addanci da su ka hada da Boko Haram da rikicin makiyaya da manoma da garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da rikicin mabiya akidar Shi’a.

Ta ce hankalin ta ya tashi matuka da abin da ta gani a Nijeriya, don haka ta ce akwai bukatar a dauki matakin gaugawa domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya, musamman a cikin shekaru goma sha biyar da su ka gabata zuwa yanzu.

Callamard, ta ce idan an bar rikicin da ke faruwa a Nijeriya ya cigaba ba tare da daukar mataki ba, lamarin zai shafi gaba daya kasashen Afrika saboda da irin rawar da Nijeriya ke takawa.

Ta ce ta yi maraba da batun gina rugage, duk da cewa shiri ne da zai dauki lokaci kafin a ci moriyar sa, tare da fatan za a gindaya matakan tsaro a jihohin da abin ya shafa idan har an kai ga matsaya.

Leave a Reply