Hukumar Alhazai ta kasa ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya.
Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.
Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce wadanda ba su fara biyan wani abu daga cikin kudin kujerar ba za su biya naira miliyan takwas, saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu.
Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kudin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiya ta ba mahajjan gwamnati yayin da ƴan kasuwa ke da kujera 20,000 wato masu tafiya ta jirgin yawo.
Hukumar ta ce tun a baya ta nemi tallafin wasu jihohi da masu hannu da shuni saboda ganin an dauke wa Alhazai ko da kudin ciyarwa ne a misha’ir da sauransu saboda abin ya zo wa alhazan da sauƙi.