Al’ummar arewacin Najeriya mazauna Legas sun gudanar da taro domin tantance irin ci gaban da suka samu da koma-baya wajen samun rabon dimokradiyya da haɗin kai.
Sun ce a yanzu sun fahimci cewa dole ne su zauna domin gano wuraren da za su inganta da kuma gyara kura-kurai na baya don tabbatar da kyakkyawar makomar al’ummar arewa mazauna Legas.
Daya daga cikin al’ummar Arewan mazauna Legas Muhammad Aminu Legas, ya ce za su yi iya bakin kokarin su wajen ganin sun hada kan al’uumar Arewan dake legas.
Domin ganin sun farfado da daraja da kuma kimar su a matsayin su na masu riko da gaskiya da amana da aka sani a can baya.
Muhammad Aminu, ya yi kira ga shugabannin Arewa a matakai daban-daban su gaggauta magance matsalolin tsaro da na kuncin rayuwa da suka yi wa Arewa katutu domin su da suke kudu a duk lokacin da suka tuna gida hankalin sun a tashi.














































