Wani malamin addinin Musulunci Sheikh Halliru Abdullahi Maraya, ya ce haɗa mabiya addini ɗaya su kasance Shugaban ƙasa da Mataimaki a ƙasa mai al’ummar Musulmi da Kirista ya saɓa wa ƙa’idar addinin Musulunci.
Sheikh Halliru Maraya, wanda tsohon mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara ne a kan harkokin addinin Musulunci, ya ce adalci shi ne a tafi tare da kowane addini wajen gudanar da mulkin ƙasa.
Shaihin Malamin ya kara da cewa, a harkar mulki gaba daya ba abin da ya ke sa a samu a nasara illa a yi adalci.
Ya ce, addinin Musulunci addini ne da ya ke so a ko da yaushe a yi ma wadanda ba su yin sa adalci a kuma kyautata masu, ma’ana a ba kowane mai hakki hakkin sa.
Sheikh Halliru Maraya, ya ce Nijeriya ta Musulmi ce da wadanda ba Musulmi ba, don haka bangarorin biyu su tabbatar cewa sun yi wa juna adalci.














































