Home Labarai Gyaran Masarautu: Ana Zaman Jin Ra’ayoyin Jama’a A Sakwato

Gyaran Masarautu: Ana Zaman Jin Ra’ayoyin Jama’a A Sakwato

73
0
Front of Sokoto Sultan Palce
Front of Sokoto Sultan Palce

kwamitin da Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta miƙa wa ƙudurin dokar gyaran fuska ga masarautu ya fara zaman sauraren ra’ayin jama’a.

Tun da farko gwamnatin jihar ta ce za ta yi gyara ne ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar ta shekarar 2008.

An riga an yi wa dokar karatu na farko da na biyu a wani zama da aka yi ranar Talatar makon jiya,

inda ake sa ran da ƙudurin ya zama doka, ƙarfin ikon nadawa da cire hakimai da dagatai zai koma ƙarƙashin ikon gwamnan jihar Sokoto, maimakon Sarkin Musulmi.

 Sai dai lamarin na ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda jama’a da dama a Najeriya suka bayyana matakin da shirin rage ƙarfin ikon Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.

Daga cikin waɗanda suka mayar da martini har da ƙungiyar kare hakkin Muslumi ta Najeriya wato MURIC,

da ta bayyana cewa taɓa kimar Sarkin Musulmin tamkar taba ruhin Musulman Najeriya ne.

Leave a Reply