Gwamnonin Kudu maso Gabas da sauran shugabannin kabilar
Igbo na shirin ganawa da shugaba Tinubu a kan matsalar
rashin tsaro a yankunan su kamar yadda Gwamna Hope
Uzodinma na jihar Imo ya sanar.
Gwamnan Hope Uzodinma ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar sa da ke Abuja.
Uzodinma, ya ce shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na Kudu maso Gabas da shugabannin kabilar Igbo sun yanke shawarar ganawa da shugaban kasa a kan matsalar rashin tsaro a yankin.
Ya ce ya je fadar shugaban kasa ne domin samun ganawa da shugabannin yankin kudu maso gabas da shugaba Tinubu.
Gwamnan Uzodinma, ya ce kowa ya san yankin Kudu-maso- gabas an yi ta fama da matsalolin ‘yan fashi, da sace-sacen ‘yan bindiga.