Home Labaru Gbajabiamila Zai Jagoranci Kwamitin Shugabannin Hukumomi

Gbajabiamila Zai Jagoranci Kwamitin Shugabannin Hukumomi

54
0

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya nada Femi Gbajabiamila a
matsayin jagoran kwamitin da aka dora wa alhakin cike
gurbin shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da aka
rushe.

Kwamitin dai, shi ke da alhakin kafa tsarin zaben wadanda za a nada a mukaman, daidai da tanadin doka da cancantar wadanda za a nada a Ma’aikatu da Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati.

Shugaba Tinubu ya dora wa kwamitin alhakin nazari a kan hukumomin da dokar kafa su ta tanadi ainahin matakin karatun da sai mutum ya kai domin samun matsayin.

Daga cikin ‘yan kwamitin kuwa akwai sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume, da mai ba shugaban kasa shawara ta musamman a kan harkokin siyasa da gwamnatoci Mallam Yau Darazo, da wasu masana harkokin shari’a da kamfanoni masu zaman kan su.

Leave a Reply