Home Labarai Apc a Bauchi Ta Dakatar Da Shugabanta a Matakin Gunduma Kan Yi...

Apc a Bauchi Ta Dakatar Da Shugabanta a Matakin Gunduma Kan Yi Wa Jam’Iyya Zagon Ƙasa

68
0

Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, ta dakatar da shugaban
jam’iyyar na jihar Alhaji Babayo Aliyu Misau bisa zargin yi
wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Gundumar Kukadu Gundari da ke yankin Ƙaramar Hukumar Misau ce ta dakatar da Babayo Aliyu, bayan ta zarge shi da aikata wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Shugabannin jam’iyyar Gundumar Kukadu a ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Zango Lawan, da Sakataren sa Aliyu Hassan Adamu da Mataimakiyar shugabar mata Asabe Ahmed su ka bayyana sanarwar dakatarwar ga manema labarai.

Sun ce sun kira taron gaugawa a ranar Juma’ar da ta gabata, inda a nan ne su ka yanke shawarar dakatar da Babayo bayan nazari a kan laifuffukan da ya aikata ciki har da yi wa jam’iyya zagon ƙasa.

A cewarsu, an samu Babayo da aikata wa jam’iyya zagon ƙasa kafin da lokacin da kuma bayan zaɓubbukan da su ka gudana kwanan baya.