Home Labaru Gwamnatin Tarayya Na Duba Yuwuwar Saka Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Anambara

Gwamnatin Tarayya Na Duba Yuwuwar Saka Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Anambara

20
0

Gwamnatin taraya ta nuna Al’amun cewa mai yuwuwa ta sanya dokar ta-ɓaci a jihar Anambra dake kudu maso gabashin ƙasar nan idan aka ci gaba da kashe-kashen da ake yi a jihar.

Gwamnatin ta sanar da haka ne a wani mataki na tabbatar da an yi zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

Babban lauyan gwamnatin tarayyar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ne ya bayyana alamun haka a lokacin da yake jawabi ga ƴan jarida a ƙarshen taron Majalisar zartarwa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce za su iya ɗaukar kowane mataki ciki har da sanya dokar ta-ɓaci a ƙoƙarinsu na tabbatar da an yi zaɓen cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Ya ƙara da cewa a matsayinsu na gwamnati alhaki ya rataya a wuyansu na su tabbatar da ɗorewar tsarin dumokuraɗiyya kuma su tabbatar da tsaro ga lafiya da dukiya.