Home Labaru Rikicin Dan Takara Na Barazana Ga Hadin Kan PDP

Rikicin Dan Takara Na Barazana Ga Hadin Kan PDP

16
0
PDF

Takaddama ta kaure a jam’iyyar PDP bayan kwamitin raba muƙaman ya keɓe wa yankin arewacin Najeriya kujerar shugaban jam’iyya.

Wannan dai wata alama ce da ke nuna cewa bangaren kudu ne zai fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Azantawarsa da kafar yada labarai ta BBC Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ibrahim Tsauri, yace zai tattauna a kan maganar rabon mukamai.

Kwamitin raba mukaman wanda gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ke jagoranta ya ba da shawarar a gudanar da sauye-sauyen.

Tuni dai kebe wa arewacin Najeriya kujerar shugaban jam’iyyar ya fusata wasu jiga-jigan Jam’iyar yayin da wasu ke ganin an yi hakan ne da kyakkyawar manufa.

Anasa bangaren tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce suna nazari akan yadda kwamitin zartarwar ke gudanar da aikinsa.