Home Labarai Gwamnatin Nijeriya Ta Kuduri Kawar Da Amfani Da Kananzir Nan Da 2030

Gwamnatin Nijeriya Ta Kuduri Kawar Da Amfani Da Kananzir Nan Da 2030

55
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce za a yi duk mai yiwuwa domin ganin ‘yan Nijeriya sun daina amfani da makamashin kananzir da itacen girki daga shekara ta 2030.

Buhari ya ce wannan wani bangare ne na tsare-tsaren gwamnatin sa na rage azababben hayaki mai gurbata muhalli.

Shugaba Buhari, ya ce an mika hukumar NDC mai alhakin kula da aikin ne domin maye gurbin gudunmawar wucin-gadi tsakanin Nijeriya da majalisar dinkin Duniya.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya raba wa manema labarai.

Ya ce Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata ganawar bidiyo da shugaban kasar Amurka Joe Biden, inda ya ce gwamnati za ta tabbatar da maye gurbin kananzir da itace da iskar gas na girki domin rage gurbatar yanayi da iska a Nijeriya.