Home Labaru Ilimi Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Makarantun Firamare Da Sakandare Hutu

Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Makarantun Firamare Da Sakandare Hutu

1
0

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, ta amince makarantun
firamare da sakandare da ke faɗin jihar su tafi hutun ƙarshen
zango na biyu da watan Ramadan daga ranar Alhamis, 7 ga
watan Afrilu na shekara ta 2023.

Gwamnatin jihar Kano, ta yi kira ga iyayen ɗaliban da ke makarantun kwana su je su kwashi ‘ya’yan su a ranar Juma’a da safe.

Bayanin hakan ya na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar ta fitar ta bakin Daraktan Wayar da Kan Jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf.

Aliyu Yusuf, ya ce ana sa ran ɗaliban da ke makarantun kwana su koma hutu ya zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, yayin da ‘yan je-ka-ka-dawo za su koma a ranar 1 ga watan Mayu.

Ma’aikatar ta yi kira ga iyayen ɗalibai da su kula da ranakun komawa makaranta da aka tsaida, domin a ba ɗalibai damar komawa makaranta a kan lokaci, sannan ta yi gargaɗin za a ɗauki matakin ladabtarwa a kan duk ɗalibin da ya saɓa lokacin komawa makaranta.