Home Labarai Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Maida ‘Yan Hisbah Cikakkun Jami’an Tsaro

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Maida ‘Yan Hisbah Cikakkun Jami’an Tsaro

357
0

Gwamnatin jihar Kebbi ta maida jami’an Hukumar Hisbah cikakkun jami’an tsaro.

Mai magana da yawun Gwamna Abubakar Bagudu Yahaya Sarki, ya ce Gwamnatin jihar Kebbi da ‘yan Majalisar Dokoki na Jihar da Shugabannin Ƙananan Hukumomi sun ba hukumar Hisbah gudummawar tallafin naira miliyan 100 don su ji daɗin gudanar da aikin su.

Ya ce hukumar Hisbah ta taka muhimmiyar rawa wajen kauda alfasha a faɗin Jihar Kebbi, musamman a ɓangaren shaye-shayen giya da karuwanci.

Gwamna Bagudu, ya ce namijin ƙoƙarin da hukumar Hisbah ta yi tsawon shekaru 20 da kafuwa a jihar, shi ya sa gwamnatin jihar ta ga ya dace kuma lokaci ya yi da za a maida hukumar Hisbah cikakkun jami’an tsaro.

Ya ce ayyukan ta ba su tsaya a kan hana aikata alfasha da shan giya da karuwanci kaɗai ba, Hisbah ta yi nasarar cusa wa matasa ɗa’a da ɗora al’umma a kan hanya madaidaiciya.

Leave a Reply