Home Home Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Kisan Mutum 12 A Kajuru

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Kisan Mutum 12 A Kajuru

30
0

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla kimanin mutane 12 hade da kona gidaje kusan 20 a wasu kauyukan jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a a ƙauyen Gindin Dutse Makeli da ke karamar hukumar Kajuru, kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun kashe mutane shida tare da sace wasu 60 a kauyukan Kwassam da Sabon Layi a karamar hukumar Kauru.

Kwamishinan riƙo na tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce yanzu haka jami’an tsaro na yin iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun shawo kan lamarin.

Aruwan ya ce lamarin bai yi wa gwamnatin jihar daɗi ba kuma tuni su ka aika da ta’aziyyar su ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa babu wani bayani da ke nuna cewa maharan sun yi garkuwa da wasu mutanen a kauyen bayan kai harin.

Leave a Reply