Home Labaru Gwamnatin Jihar Bauchi Za Ta Ɗauki Likitoci Sama Da 1000 Aiki A...

Gwamnatin Jihar Bauchi Za Ta Ɗauki Likitoci Sama Da 1000 Aiki A Jihar

145
0

Shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar Bauchi Yahuza Haruna, ya ce gwamnatin jihar za ta dauki dalibai likitoci dubu 1 da 61 aiki.

Yahuza Haruna ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin inganta fannin kiwon lafiya da inganta karfin ma’aikata a jihar Bauchi.

Ya ce za a tabbatar da matsayin kowane likita kafin a ba shi wasikar daukar aikin sa.

Yahuza Haruna ya kara da cewa, gwamnati za ta dauki daliban da su ka kammala karatu a fannin kula da dabbobi domin a ba su aikin yi a ma’aikatar noma, lamarin da ya ce ya na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin sama wa matasa aikin yi a jihar.

Wata majiya ta ce, ɗaliban da gwamnati za ta ba aikin dalibai ne daga makarantun horar da ma’aikatan jinya da Ungozoma da kwalejin koyar da kiwon lafiya da fasaha da ke jihar, wadanda ke aiki ba tare da ana biyan su albashi ba.