Home Labaru Gwamnatin Buhari Ba Za Ta Yanke Huldar Jakadanci Da Afirka Ta Kudu...

Gwamnatin Buhari Ba Za Ta Yanke Huldar Jakadanci Da Afirka Ta Kudu Ba – Geoffrey

251
0
Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya
Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama ya ce Nijeriya ba za yanke huldar jakadanci da Afirka ta Kudu ba, duk da nuna tsanar da aka yi wa ‘yan Nijeriya a kasar.

Onyeama, ya bayyana haka ne a lokacin da ya tabbatarwa  kwamitin majalisar dattawa da aka kafa a kan a tsanar da aka yi wa ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu.

Ya ce, kididdiga ta nuna cewa, akwai ‘yan Nijeriya sama da 800,000 da ke da izinin zama a kasar, saboda haka matukar Nijeriya ta yanke huldar jakadanci tsakanin ta da Afirka ta Kudu, hakan zai shafi rayuwar wadannan ‘yan Nijeriya musamman ayyuakan su na da kulum da kuma harkokin kasuwancin su.

Ministan ya kara da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawaga ta musamman wadda za ta je kasar  a Asabar din nan domin dawowa da sahihan  bayanai.

Onyeama ya ce, rahoton da suka zo da shi, za a yi amfani wajen daukar matakin da ya dace, sannan kuma  ba sa tunanin yanke huldar jakadanci domin kuwa akwai hanyoyi da dama wadanda za a iya bi domin warware wannan matsala.