An kwantar da wani dalibin jami’ar Ebonyi a asibiti mai suna Ikechukwu Oke sakamakon ya shafe kwanaki 41 yana azumi da addu’o’i.
Dalibin da yanzu haka ya ke kwance a asibiti, ya ce ya fara wannan azumi ne saboda irin matsalolin da iyayen shi suke ciki a ‘yan kwanakin nan.
Wani mai suna Christian Nwaokpa ya sanarwa manema labarai cewa, dalibin dan kauyen karamar hukumar Ezza ta arewa ne kuma dama can haka ya ke irin wannan azumin.
Izuwa wannan lokaci dai wasu mutane sun dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Abakaliki domin cigaba da duba lafiyar sa.