Home Labaru Gwamnatin Bauchi Ta Warware Rawunan Wasu Hakimai 6

Gwamnatin Bauchi Ta Warware Rawunan Wasu Hakimai 6

48
0

Hukumar kula da kananan hukumomi ta jihar Bauchi, ta
warware rawunnan wasu Hakimai 6 daga Sarautun su bisa
zargin su da shiga harkokin siyasa dumu-dumu.

Wata maijya ta ce, Hakiman da lamarin ya shafa sun fito ne daga Masarautar Bauchi da Katagum.

Babban sakataren hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi na jihar Bauchi Nasiru Ibrahim Dewu ya bayyana wa manema labarai haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce Hukumar ta amince da warware rawunan wasu sarakuna shida daga masarautun Bauchi da Katagum, saboda shiga harkokin siyasa da kuma samun su da laifuffukan da su ka hada da rashin da’a, da sare itatuwa, da almubazzaranci da dukiyar al’umma da rashin bin doka da oda.

Nasiru Ibrahim Dewu, ya ce masu rike da Sauratun da abin ya shafa sun hada da Hakimin Dubi Aminu Muhammed Malami, da Hakimin Azare Bashir Kabir Umar, da Hakimin Tafiya Umar Omar sai kuma Hakimin Tarmasawa Umar Bani.

Wadanda abin ya shafa daga Masarautar Bauchi kuma sun hada da Hakimin Beni Bello Sulaiman da Hakimin kauyen Badara Yusuf Aliyu Badara.

Dewu ya kara da cewa, an umurci sarakunan da aka kora su mika ragamar yankunan su ga sakatarorin su.

Leave a Reply