Gwamnatin Najeriya ta bayyana matakan da take dauka na hana tilasta wa likitocin ta yin ƙaura zuwa kasashen waje.
Wannan dai wata sabuwar manufa ce ta gwamnatin shugaban kasa Tinubu domin kawo sauyi game da yadda ake tafiyar da al’amurran ma’aikatan.
A cewar gwamnatin tana fatan wannan manufa za ta magance manyan matsalolin da ke tilasta wa ma’aikatan kiwon lafiya na Najeriya yin ƙaura zuwa kasashen waje.
Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate ya shaida cewa gwamnatin su na sane da yadda likitoci da ma ma’aikatan lafiya ke yin ƙaura zuwa ƙasashen.
Ya ce tsari ne da zai taimaka wajen ƙara yawan likitoci da ma’aikatan lafiya, ba tare da ya hana masu son tafiya kasashen waje zuwa ba,
amma manufar ita ce bayar da dama ga waɗanda suke ƙasashen waje su dawo gida Najeriya domin su taimakawa wajen inganta kiwon lafiya a kasar su.














































