GWAMNATI ZA TA BINNE GAWARWAKI 49 A RAMI GUDA A KADUNA
Gwamnatin Jihar Kaduna, ta ce za ta birne wasu gawarwaki 49 a rami daya idan ‘yan’uwan su ba su je sun tafi da su ba.
Ta ce za ta yi hakan ne bayan wa’adin kwanaki biyar da ta ba dangin mamatan su dauke su daga ma’ajiyar gawarwaki ta Babban Asibitin Sabon Tasha da ke Karamar Hukumar Chiku.
Shugaban Karamar Hukumar Chikun Salasi Nuhu Musa, ya ce an kai gawarwakin asibitin ne a lokuta daban-daban daga ofishin ‘yan sanda na Kasuwar Magani da na Toll Gate.
Ya ce an iya gane 25 daga cikin gawarwakin 49, ragowar 24 kuma ba a gane su ba saboda ba su dauke da wata alamar shaida lokacin da aka kai su asibitin.
Salasi Nuhu Musa ya kara da cewa, tuni karamar hukumar ta samu amincewar gwamnatin jihar domin birne gawarwakin, wanda zai gudana a mako mai zuwa.














































