Home Labaru Gwamnati Na Za Ta Kawar Da Matsalar Tsaro – Tinubu

Gwamnati Na Za Ta Kawar Da Matsalar Tsaro – Tinubu

314
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya na sane da
matsalar tsaron da ake fama da ita a Nijeriya, tare da shan
alwashin cewa zai magance ta gaba daya.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin gudanar da bikin Ranar Sojoji a jihar Oyo, inda ya samu wakilcin mataimakin sa Kashim Shettima.

Shugaba Tinubu ya sha alwashin cewa, gwamnati za ta shawo kan matsalolin harkokin tsaro a cikin kankanen lokaci, ya na mai jaddada cewa za a bada cikakkiyar kulawa ga sojojin Nijeriya, musamman matsalar rashin kuɗi da ta makamai.

Tinubu ya ce gwamnati ta ɗauko dabarun magance matsalolin da ake fama da su, sannan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su kauce wa duk wani abin da zai iya raba kan al’umma.

Leave a Reply