Home Labarai Gwamnan Ondo Ya Umarci A Kori Ma’aikatan Dake Karɓan Albashi Biyu

Gwamnan Ondo Ya Umarci A Kori Ma’aikatan Dake Karɓan Albashi Biyu

15
0

Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu, ya umarci shugabar ma’aikata ta jihar ta rubuta takardar sallama ga duk jami’in gwamnatin da aka gano ya na karɓar Albashi fiye da ɗaya.

Akeredolu ya bada umarnin ne yayin da ya karɓi rahoton kwamitin bincike da bin ƙwakkwafi da sharar jerin ma’aikatan da ake biya Albashi.

Gwamnan, wanda ya yi zargi cewa, tsarin da ya haɗa da masu karɓar albashi da Fansho an gurɓata shi, don haka ya kafa kwamitin mutane bakwai domin su binciki ma’aikatan da ke kan tsarin.

Kwamitin a kasrkashin jagorancin tsohon Sakataren dindindin na ma’aikatar kuɗi ta jihar Mista Victor Olajorin, ya miƙa rahoton binciken da ya gudanar ga gwamnan a Ofishin sa da keAkure.

Da yake karɓar rahoton, Gwamna Akeredolu ya jijjiga da ganin abubuwan da aka bankaɗo, kuma ya koka da nauyin ma’aikata fiye da ƙima, wanda a cewar sa ke tattare da ma’ikatan bogi.