Home Labarai Atiku Yana Ganin Buhari Ya Yi Abin Da Ya Cancanci Yabo, Ya...

Atiku Yana Ganin Buhari Ya Yi Abin Da Ya Cancanci Yabo, Ya Jinjinawa Shugaban Kasa

103
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yaba da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na maida NNPC kamfanin kasuwanci.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce matakin da aka dauka ya na daga cikin manufofin sa, domin ganin an yi garambawul ta yadda gwamnati za ta rika cin riba sosai.

Wazirin Adamawa, ya kuma bada misali da kasar Saudiyya,
wadda ta saida kamfanin man ta na Aramco da Petrobras da
kasar Brazil ta ba mutane damar zuba kudin su.

Ya ce a shekara ta 2018, ya shaida wa duniya kudirin shi na gyara kamfanin NNPC ta yadda zai rika cin riba sosai, da kuma tabbatar da gaskiyar keke-da-keke, amma gwamnatin APCta yi ma shi kaca-kaca saboda hangen nesan shi na kishin-kasa.

Atiku Abubakar, ya ce yay i murna da wannan gwamnatin ta kama hanyar shawarar da ya bada, domin matakin aka dauka ya yi kyau, sai dai ya ce har yanzu akwai sauran aiki a kan abin da ya ke son aiwatarwa.